Aisha Humaira Jarumar Kannywood Tace Duk Masoyinta Ya Zabi Gawuna A Jihar Kano – Interestingasf

Ina bawa duk Wani masoyina Umarni ya Zabi Dr. Nasiru Yusuf Gawuna Ranar Zabe, da za’a gudanar a garin kano state dake nigeria cewar jarumar fina finan hausa ta kannywood Aisha Humaira.

Aisha humairah ta kara dacewa duk wanda yasan masoyina ne kuma idan na isa dashi inaso ya zabi Dr. Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin Gwamnan jihar Kano domin ya dora daga inda baba ganduje ya tsaya da aikin jihar mu ta kano.

Idan kuka zaÉ“e shi, zai maida Kano gari mai kyau wataran ma har yawon bude ido za’a rinÆ™a zuwa Kano saboda kyau idan aka zabe shi, nayi imanin cewa saiya mayar da garin kano abin alfahari a cikin kasar nan dama duniya baki daya.

Za’a gudanar da zaben gwamnan jihar kano ranar asabar mai zuwa ta cikin wannan mako don haka inaso ku zabi gawuna domin shine kadai mutumin da yafi dacewa daya mulki jihar kanon mu ba mutanan da basa kishin jihar mu ba.

Aisha hunairah jarumar Fina finan hausa ta kasance daya daga cikin tawagar yakin neman zaben dan takarar gwamna na jihar kano sannan kuma itace ta hannun daman babban mawaki siyasar (APC) wanda akafi sani da dauda kahutu rarara wannan dalilin yasa tayi wannan maganar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *