ADDU’AR DAREN LAILATUL QADRI

Wannan ita ce addu’ar da Manzon Allah, sallallahu alaihi wa sallama, ya koyar da Nana A’isha, Radhiyallahu anhaa, ta rinƙa yi a daren LAILATUL QADRI, wato

“اللَّهُمَّ إِنَّكَ عَفُوٌّ كَرِيمٌ تُحِبُّ الْعَفْوَ فَاعْفُ عَنِّي”.

Allahumma innaKa ‘Afuwwun, tuhibbul’ afwa fa’fu ‘anniy.

Wannan addu’a ta ƙunshi alherin duniya da lahira.

Don haka yana da kyau a yi ƙoƙari a haddace musamman yanda muke fuskantar goman ƙarshe na Ramadana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *