Kina fama da kaikayin gaba, kuraje, fitar da ruwa mai wari?
Kashi tamanin (90%) cikin dari (100%) na sanyin gaba bashi da alaka da jima’i.
Kamar yadda mutum yake wanke bakin sa (brushing) haka ya kamata mace kullum ta canza under wear nata.
Barin under wear a jiki fiye da kwana daya yana haifar da:
Kaikayi gaba
Warin gaba
Fitar da ruwa
Kuraje
kada a hada wankekken under wear da kaya masu datti.
Ayi kokorin siyan under wear wanda akayi shi da auduga (cotton), a kiyaye amfani da na roba (nylon).
Gaban mace baya bukatar a wanke shi da sabulu, ayi amfani da ruwan dumi ( ba mai zafi sosai ba).
Lokocin al’ada a dinga canza auduga (pad) akai akai (a kalla so biyar a wuni).
A dinga shan ruwa akai akai domin yana taimaka wajen bada kariya.