Abubuwan Da Suka Dace Uwa Ta Sanarwa ‘Yarta A Lokacin Tasowarta:

Abubuwan Da Suka Dace Uwa Ta Sanarwa ‘Yarta A Lokacin Tasowarta:

Akwai abubuwa da dama da suka dace duk uwa ta tabbatar ta sanarwa ‘yata musamman a lokacin da ta soma zama mace.

Wadannan abubuwan zasu taimakawa diya mace wajen sanin yadda rayuwa yake.
Ga wasu abubuwan da suka kamata duk uwa ta sanarwa’yata.

1: Yana da kyau duk uwa ta nunawa ‘yarta tare da sanar da ita mahimmancin da illimi yake dashi a rayuwarta.

Sanarwa diya mace mahimmanci illimi na addini dana zamani zai baiwa diya mace kwarin gwaiwa da zata maida hankalin ta domin ganin ta samesu.

Dole ne uwa ta nunawa ‘yarta a wannan lokacin da ake ciki babu macen da take da daraja cikin al’uma sai idan tana da illimi.

2: Uwa ta nunawa ‘yarta cewa, yanada kyau idan an mata ba dai-dai ba tayi magana. Idan an mata daidai nan ma tayi magana.
Rashin nunawa ‘ya mace hakan yasa ake cutarwa da ‘ya’ya mata kuma su kasa magana. Ko kuma a musu abun arziki basu iya nunawa godiyarsu ba.

Nunawa diyarki duk wanda yayi mata ba daidai tanada damar ta masa magana amma cikin girmamawa. Haka nan duk kankantar abun kwarai da aka mata ta nuna farin cikinta da godiya ga wanda suka mata. Kada ta zama mara magana kada kuma ta zama mara godiya.

3:Nunawa ‘yarki a rayuwa akwai samu kuma akwai rashi. Sanar da ita hakan zai fahimtar da ita rayuwa.
Idan yarki tana cikin wadata ne, ma’ana iyayenta nada wadata. Dole ne a nuna mata cewa akwai miliyoyin mutane da yanzu haka suke kwana da yunwa. Akwai kuma masu wadatar da har zubba abinci suke. A nuna mata alherin dake cikin taimakawa marasa shi. Da kuma yiwa Allah (SWT) godiya ako wani yanayi mutum ya samu kansa.

4: Ki nunawa ‘yar ki yadda zata mutunta mutane. Yadda zata daraja mutane.
Nuna mata ba wasu sun fi wasu bane saboda Allah baya son marasa shi bane. Kawai haka tsarinsa yake.
Ta kuma sani marashi a yau na iya samu a gobe. Don haka duk wani mutum data gani ta mutuntashi ta daraja shi.

5: Kada ki boyewa ‘yarki sanin tarihi da kaita asalin tushenta. Duk wata uwa, dole ne ta nunawa ‘yarta cewa sunada asali, koda kuwa talauci ko kaskanci ne a asalin nasu.

Uwar da zata nunawa ko ta sanarwa ‘yata wadannan abubuwan ko makamantansu, dole ne diyarta ta taso cikin tarbiya da sanin ya kamata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *