Abubuwan da ke kawowa mata ciwon nono

Wato Sanqaran Mama ko kuma Kansar mama. shi ne samuwar wasu kwayoyin cuta acikin nonon mace, wandanda ke haddasa ciwo da canja yanayin nonon mace ko ya lalata shi gaba daya. Ciwon nono wani lokacin yana janyo ru6ewar nono ko yay sanadin a yanke shi gaba daya.

YADDA AKE DAUKAR CIWON
Abubuwan da ke kawowa mata ciwon nono.

Shekaru ko tsufa.
Idan mace shekarunta suka dan fara yawa, to yana da kyau ta fara daukar matakan kariya daga ciwon nono.

Sinadarin ‘iyistirogen’, idan yay yawa ajikin mace.

Fara jinin al’ada kafin mace ta kai shekaru sha biyu, za ta iya gamuwa da ciwon nono daga baya.

Mace ta zarce shekaru hamsin da biyar tana jinin al’ada, shi ma zai iya janyo mata ciwon nono.

Rashin haihuwa. Matan da sam ba su haihu ba, har su ka wuce shekaru talatin, za su iya kamuwa da ciwon nono.

Jinkirin haihuwa.
Idan mace ta dauki shekaru da yawa da aure ba ta samu haihuwa ba za ta iya kamuwa da ciwon nono.

Girman jiki.
A binciken likitoci, mace mai tsawo da mace mai kiba, sun fi shiga hadarin kamuwa da ciwon nono, musamman masu tarin kitse a jikinsu ko a kugunsu.

Gado.
Idan iyayen mace suna fama da ciwon nono, to itama zai iya yiwuwa ta yi gado.

Idan nonon mace guda daya ya ta6a yin ciwo, to zai iya yiwuwa dayanma ya kama ciwo daga baya.

Matar da aka ta6a cire mata tsiro a mamanta, yana da kyau ta dinga zuwa asibiti tana samun shawarwari don gudun kamuwa da ciwon nono daga baya.

ALAMOMIN CIWON NONO

Canjin yanayin girman nono.
Haka kawai ki ga nononki yana kara girma ko ya yamutse, ba tare da wani dalili ba.

Jin kullutu acikin nono.
Za ki ji kamar wasu abubuwa suna tsirowa daga nononki, har suna kara girma.

Canjin kalar fatar nono. Za ki ga fatar nonon tana komawa kamar yalo-yalo ko jaja-jaja ko wata kala daban.

Canjin kalar fatar kewayen nono (nipple), ki ga fatar wajen ta yi jajawur.

Kan nonon mace (nipple) ya zama ya kumbura haka kawai

kuma yana ciwo.

Fitar wani ruwa kamar ruwan ciwo haka kawai daga nonon mace. Ba sai lallai matar aure ba, ko da budurwa ce.

Radadi da ciwo mai zafi akan nonon da kuma hammata ko da yaushe kuma haka kawai.

Kumburin hammata tsakanin allon kafada zuwa sashin nonon.

Jin ciwo mai tsanani idan kika matsa nonon.

Nan zan tsaya

insha allahu nan gaba idan dama tasamu zan Cigaba da bayani kan wannan lalura

Allah ya karemu da iyalanmu daga wannan lalura

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *