ABUBUWAN DA AKAFI SO MACE MAI JUNA TA RIKA AIKATAWA DOMIN SAMUN YARO NAGARI

Daga mu gyara mata

Wadannan wasu abubuwa ne da ake so mace mai juna pregnant woman ta daure ta rika kiyayewa, domin samun yaro ko yarinya kai kyakkyawar dabi’a, da addini da sauran dabi’u da kowanne uba yake so yaransa su kasance domin kyautata mutumtaka ta iyali.

Ana so mace mai juna ta kasance ko da yaushe tana da alwala, musaman lokuta na cin abinci, yakasance tana cikin alwala.

Anaso mace mai juna ta kasance tana yawan kallon alqibla Gabas, yayin gudanar da ayyukanta na yau da kullum. Musaman cin abinci da shan ruwa.

Anaso mace mai juna ta kasance kullum tana yin sadaka, da niyyar Allah ya kare mata lafiyarta da ta jaririnta.

Ba’a so mace mai juna ta rika kallon madubi mirror da dare.

Anaso mace mai juna ta kiyaye kanta daga aikata munafurci, da kuma karya.

Anaso mace mai ciki ta rika kiyaye dukkan abubuwan da yazama wajibi a matsayinta na musulma. Ta kuma dage wajan aikata abubuwan da suke abababen so, kamar kiyaye farilla da kuma aikata sunna.

Anaso koda yaushe mace mai ciki ta kasance cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, ta kasance tana yin tunanin abu mai kyau kuma ta kiyaye yin fushi.

Anaso mace mai ciki ta kiyaye dukkan damuwa akan yanayin da jaririnta yake koda ta samu wani bayani akan halinta jaririn nata yake ciki, ta dogara ga Allah ta barwa Allah komai.

Anaso mace mai ciki ta saurari kuma ta yawaita karanta al’qur’ani iya iyawarta, domin hakan na taimakawa wajan yaro yakasance mahaddacin al’qur’ani kuma mai son karanta al’qur’ani.

Ta dunga saurarar wa’azi na mallamai na addini.

Anaso mace mai ciki ta kasance ta rika yin wankan juma’a duk sati na tsawon sati 40, ciki yana daukar sati 40 kafin mace ta haifeshi. Ya zo a ruwaya cewa idan mutum yayi wankan tsarki a juma’a 40 a jere, to Allah zai yaye masa tsanani matsewar kabari.

Anaso mace mai ciki tayi sallar dare akalla sau 40, idan bazata iya tashi kafin sallar asuba tayi nafila ba, zata iya gabatarwa bayan sallar isha’i.

Anaso mace mai ciki taci raisin nansan sunansa da hausa ba, na kwana 40 kullum kafin taci komai da safe. Kullum taci guda 21, kuma anaso tayi Bismillah kafin tasa kowanne daya a bakinta.

Anaso mace mai juna ta rika yawan ambaton Allah.

Anaso mace mai ciki ta rika taimakawa mabukata.

Anaso ta yawaita kallon fuskar bayin Allah da kuma kallon abubuwa masu kyau kamar fulawa fure.

Kada ta rika yawan zama da mutane marasa kyakkyawar dabi’a.

Ta rika yin ziyara.

Anaso mace mai ciki ta rika yawan yin Salatin Annabi (SAW)

Anaso ayiwa yaro ko yarinya suna tun suna ciki, kuma anaso a rika sanya musu sunaye masu kyau kamar Muhammad, Ali, fatima da sauran sunaye kuma a rika kiransu da wadannan sunaye.

Anaso a rika yawan magana da yaron da yake ciki kafin a haifeshi domin hakan na kara shaquwa tsakanin iyaye da yaro, koda an haifeshi zai kiyaye wannan a kwakwalwarsa bazai manta ba.

Wadannan bayanai mun ciro su ne a cikin littattafan addini domin inga rayuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *