ABUBUWAN BIRGEWA GAME DA MATA

ABUBUWAN BIRGEWA GAME DA MATA

A ci gaba da kawo muku wasu bambamce bambamce na halittu dana dabi’a tsakanin Maza da Mata Yau ma ga wasu abubuwan burgewa na halita game da mata da yawancin maza basu sansu ba

Mace tana cikin tsananin damuwa amma da zaka tambayeta yaya take zata ce maka lafiya take batada matsala

Haka kuma idan mace ta fito fili ta fadamaka matsalata ba tana fadamaka bane domin ka taimaka mata ba sai domin ta aminta dakai ne tana neman kalmar da zai kwantar mata da hankali daga gareka

Mata sunada zurfin ciki hakan yasa muddin namiji bazai yi amfani da yakamata ba zai jima yana kuntatawa matarsa kanwarsa budurwar sa ko mahaifiyarsa bai sani ba

Mata suna fadawa mutumin da suka yarda dashi kuma sukasan zai biya musu bukatunsu na matsalar su ne amma ba kowa ba

Mata a kowani lokaci a kowani yanayi suna cikin bukata ne Hakan yasa mata sun fi maza yawan tunani

Mata sukan dauki matsalolin daba nasu ba su daurawa kansu Haka nan suna son yin rayuwa fiye da samunsu Wannan yasa a kullum cikin bukata suke a kullum cikin matsala da damuwa suke

Duk wata mace tana daukan kanta kyankyawa ce
Amma kuma kashi 2 ne cikin 10 na mata suke fitowa gaban mutane suyi ikirarin suna da kyau

Duk kyau mace idan kace mata tanada kyau sai taji dadi a ranta Haka duk munin mace ta tsani ka ce mata mummuna amma ita tana iya fadawa kanta da kanta ita mummunace amma da wani zai fadamata bazata so ba

Mata sunfi yawan tunanin ko kuma son kusanci da mutanen da basu damu dasu ba

Ga inda ake tarairayan mace tafi so taje inda itace zata yi tarairayan

Mace ta tsani ka kwatanta da wata macen Ka nuna wacce ta fita da wani abun Amma mace ita da kanta zata iya fadamaka wacce ta zarce mata a wani abun

Idan sune suka fada da kansu hakan bai musu zafi maimakon wani ya nuna cewa wata ta fita

Mata sunfi maza dauriya idan suna ciwo Hakan yasa sukafi maza yawan lalura

Da Allah Ya halicci mata da yawan laulayi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *