Abubuwa guda 4 dasuke matuqar jawo hankalin namiji yaso matarsa so matsananci:

  1. tsafta: kowanna namiji yana matuqar son tsafta ,kuma kowanna namiji yatsani qazanta koda shi qazamine dazarar mace tazama me tsabta hakan zaizama abun yabo agun mijinta da qaramata kima agunsa .tsafta na sa maqota ma da yan uwanki mata suso abun da kikataba ,hakanan qazanta nasa kowa yatsanaki ballantana mijinki ma.
  2. iya kwalliya: kwalliya na maida mace babba kamar budurwa hakama rashin kwalliya namai da mace kamar dodanniya ,ita mace batada wani kyau azahirinta inbatayi kwalliya ba ,sautarin rashin kwalliya nasa wasu mazan subar matansu kyawawa a gida suje neman munana a kwararo saboda sun iya kwalliya.danhaka yar uwa kikoyi kwalliya a gidan mijinki bawai sai zaki gidan bikiba. Danhaka ki tsaya kuma kikoyi yadda akeyin kwalliya mekyau ba wacce zata maidake kamar dodanniyaba alhalin komai miji yasayo yabaki.
  3. Iya girki: kowannan namiji yana alfahari da girkin matarsa yakan zuzutata akan ta iya girki koda bahakabane ,dazarar kin iya girki zakina gani mijinki na gaiyato abokansa kala kala hakan kuma naburgeshi ,na fasa masa kai .amma dazarar baki iya girkiba shima bazai naci ba sosai ballantana ma yagaiyato wasu abokansa. Dan haka lallai kizama me iya girki kala kala dan kula da mijinki.
  4. kula da haqqin kwanciya: itama wannan na daga cikin abu mafi girma dake sa mace mallake miji wato bashi haqqinsa na kwanciya aduk sadda yabuqata.hakanan kuma hana mai gida haqqinsa na kwanciya nasa miji yatsaneki yaimiki kishiya ko ma yakoreki.bayan fushin Allah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *