ABUBUWA GUDA 10 DA ZAKI MAMAYE ZUCIYAR MIJINKI DASU

Wasu matan suna dauka cewa yiwa namiji jan ido ko rashin kunya shike sa ya so su.

Akwai kuma masu daukan yawan yin Jima’i da namiji zai sa ta shiga ransa. Sai kuma basu ganin Boka ko Malam ne zasu iya sa mazansu su sosu. Duk wadannan ko da wasa basa sa miji ya so mace, ta zauna masa a zuciya yaji a duk lokacin yana matukar kewarta.

Ga wasu halaye nan guda 10 da duk macen da zata rika yiwa mijinta su dole sai yaji bai biya rabuwa da ita.

1: Nunawa Miji Yarda dari bisa dari

2: Nunawa Miji Matukar So Da Kauna

3: Yiwa Miji Shagwaba

4: Yiwa Miji Barkwanci

5: Yawan Zugashi Da Kambamashi

6: Nunawa Abunda Kuka Haifa Da Wanda Ma Bake Kika Haifa Ba Nashi Kauna

7: Nunawa Iyayensa Dana Kusa Dashi So Da Kauna

8: Yawan Masa Godiya Da Duk Kankantar Abun Alheri Da Ya Miki

9: Kada Ki Zama Mai Yawan Korafi Ko Kawo Kara

10: Karfafa Masa Gwaiwa Da Masa Fatan Alheri Ga Duk Wani Abun Alheri Daya Saka A Gaba.

Wadannan wasu daga cikin dabi’u ko halayen da mace mai burin sace zuciyar mijinta zata yi amfani dasu domin ganin ta samu rike zuciyarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *