Abubuwa 8 dake kawo jiri

Jiri wani yanayi ne dake sa mutun Jin alamun suma, ko rashin iya tsayawa atsaye,kasala ko fita daga hayyaci.

Jiri kan iyasa kaji inda kake na juyawa a wannan lokaci ko Kai kanka kaji kamar kana juyawa.

Meke kawo jiri?
Abubuwan dake sanya jiri suna da yawa. Kadan daga cikin su sun hada da:

Karancin ruwa ajiki
Karancin isasshen ruwa ajiki nadaga cikin abubuwan dake janyo jiri.
Musamman in mutun baya Shan isasshen ruwa sosai akullun.akalla ana bukatar karunka Shan Lita 3 zuwa hudu na ruwa akullun.
Cututtukan dazasu iya janyo maka karancin ruwa sun hada da amai da gudawa, malaria,sanyi na jiki(sepsis),ciwon siga da dai sauransu.
Shan ruwa na da matukar muhimmanci ajiki.

Karancin jini
Alokacin da jinin mutun yayi kasa,zairunka Jin Jiri tare da haki,faduwar gaba,yawan gumi ko ma kumburin jiki.
Abubuwan dake kawo karancin jini sun hada da zubar jini,sanyi,malaria,tsutsar ciki, cututtuka dadaddu kamar su hawan jini,ciwon Koda ko hanta da dai sauransu.

karancin sikari ajiki
Alokacin da sikarin mutun yayi kasa ajiki,zai iya fuskantar wannan matsala ta yawan jin Jiri.

Yunwa na daya daga cikin abubuwan da ke kawo karancin sikari a jiki.Yanada kyau mutun yarunka samun isasshen abinci yanaci akai akai musamman Karin kumallo Dana Rana.
Hazalika idan Yana fama da wani ciwo ajikinsa zai iya fuskantar wannan matsala ta
karancin sikari.

Fama da cututtuka dadaddu.
Fama da cututtuka na tsawon lokaci Kansa mutun yayi fama da wannan matsala.
Wadannan cututtuka sunkunshi hawan jini,ciwon siga,ciwon Koda,ciwon hanta,tsutsar ciki,ciwon daji da dai sauransu.

Matsaloli da suka shafi bangaren kunne.
Wannan sun hada da Ciwon kunne,taruwar ruwa a kunne wanda a turance ake kira da Ménière’s disease

yawa fama da ciwon kai
Yawan fama da ciwon Kai kan iya janyo maka Jiri akoda yaushe, musamman idan kadade kana fama da ciwon kan.

Matsaloli da ka iya shafan kwakwalwa.
Matsaloli na kwakwalwa kama daga su shanyewar barin jiki,Kari a kwakwalwa,Kansa ta kwakwalwa,buguwar kai da dai sauransu duk kan iya janyo maka wannan matsala ta yawan Jin Jiri.

Alokacin dakake fama da wannan matsala yanada kyau kaje wajen likitanka kutattauna sosai a tabbatar bawata matsala bace a kwakwalwarka.

Shan Magunguna
Amfani da magunguna irin na hawan jini,magungunan dakesa mutun bacci, magungunan cutar farfadiya da dai sauran su duk Kansa mutun Jin Jiri idan yakasance Yana amfani da su.

Meyakamata kayi idan kana fama Jiri da hajijiya?
Yana da kyau kaje asibiti kaga likita kayimai bayanin matsalar ka dalla dalla sannan ka amsa mai tambayoyin dazai maka.
Kafin abaka magani a asibiti,akwai gwaje gwajen da likita ka iya yi domin gano meke kawomaka Jirin.
Wasu daga cikin gwaje gwajen sun hada da:

FBC
Wannan Gwaji ne na yawan qwayoyin hallittan jini.wannan gwajin shi zai nuna ko akwai karancin jini ajikinka ko babu.

RBS
Wannan Gwaji ne dazai nuna ko akwai karancin sukari ajiki ko babu.

Hoton qwaqwalwa kama daga X ray, CT scan ko MRI
Hoton zuciya wato Echo

Magani yadanganta da abundake kawoshi Kuma a asibiti ake badashi,amma wadannan abubuwa zasu taimakawa mai Jiri:

Mutum ya kasance ya ziyarci asibiti yayin daya fuskanci wani canji a jikinsa kafin babbar matsala ta auku.

Aiki da shawarwari na likita a yayinda aka ziyarci asibiti na taimakawa matuqa.

Cin abinci me gina jiki don kariya daga qarancin jini ko sukari.

Yawaita shan ruwa musamman a lokacin zafi.

Kula da shan magunguna musamman magungunan da likita be yarje a sha ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *