- Nankarwa alama ce ta talewar fata. An fi ganinta galibi a tsatstsaye a kan fata. Kalar nankarwa ya dogara ga kalar fatar mutum.
- Akwai shimfiɗu uku da suka haɗu suka samar da fata. A likitance, nankarwa na faruwa sakamakon talewar shimfiɗar fata ta biyu.
- Galibi ta fi fitowa a kan fatar ciki. Sai dai wasu lokutan tana bayyana a kan fatar cinyoyi, nonuwa, ƙugu, damatsa da sauransu.
- Nankarwa aba ce ruwan dare. Kuma tana iya fito wa kowa, maza da mata, babba da yaro, ba sai mata masu juna biyu kawai ba.
- Waɗanda suke da sabuban fitowar nankarwa sun haɗa da:
- juna biyu: Kaso 8 cikin 10 na masu juna biyu nankarwa na fito musu.
- waɗanda suke cikin shekarun balaga.
- Wanda ya rame ko ya yi ƙiba nan da nan.
- Ga masu juna biyu, nankarwa na bajewa ko ta tsutstsuke bayan haihuwa.
- Wasu nau’in mayukan shafawa suna iƙirarin magance nankarwa, sai dai babu ƙwararan dalilai da suka tabbatar da iƙirarin nasu.
A likitance, nankarwa, musamman ga masu juna biyu, ba ta da wata matsala. Sai dai idan akwai ƙaiƙayi ko kuma damuwa game da munin da nankarwar ke haifarwa ga fata, za a iya tuntuɓar likitan fata.
Har wa yau, a tuntuɓi likita idan nankarwa ta yi faɗi sosai tare da bayyanar tarun kitse / teɓa a ciki, wuya da ƙirji domin hakan na iya zama alamun wata cutar daban.