ABINDA MAI CIKI ZATAYI IDAN CIKIN YAKAI WATA 9 DA WANDA ZAI LKCN NAKUDA

Abubuwan da Mai ciki ya kamata ta fara yi idan cikinta ya shiga wata Tara, da abinda zatayi idan ta fara nakuda.

Tabbas mata da yawa sukan sha wahala sosai idan watan ya kama domin Allah kadai ya san cikin irin yanayin da suke shiga. Wannan shafin mai albarka, ya kawo maku wata fa’ida wacce tabbas mun tabbatar da ingancin ta idan aka jaraba in sha Allah za a dace duk wata mace mai shan wahalar nakuda to ta samu Zuma mai kyau kaman cikin Kofi ko cokali 24 ta shanye a take.

Shi ya sa yana da kyau sosai da zarar cikin mace ya kai wata 7 ta dinga tafasa ‘ya’yan hulba tana zama a ciki kullum sau daya in ya shiga wata 9 ta dinga yi safe da yamma. Hakan zai taimaka sosai wajen bude kofofin aihuwa kuma da wuya mace ta karu a lokacin aihuwa. Kuma mace za ta samu garin hulba ta kwaba da Zuma tana shan cokali biyu safe da yamma, in sha Allahu za ta samu sauki sosai wajen haihuwa amma kada mace mai ciki ta yi amfani da hulba har sai cikin ya tsufa ma’ana lokacin nakuda saboda hulba tana zubar da yaron ciki

Allah Ya sa mu dace dan Allah duk wanda ya karanta to ya yi kokari ya sanar wa yan’uwa mata saboda a samu saukin nakuda sannan kuma a samu saukin fitar yaro daga cikin mahaifa Allah ya bada iko.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *