ABARBA, CITTA DA LEMUN TSAMI DON MAGANCE CUTUTTUKAN BLADDER DA MARA

A nemi abarba qwara daya wacce bata lalace ba,sai a sa wuqa a feqe 6awonta duka,dashi za a yi amfani,sai a nemi citta danya qwara daya babba,da lemun tsami qwara daya sai a yanka lemun gunduwa gunduwa.
Za a hadesu waje daya da fatar abarba da citta da lemun Tsamin duka a waje daya sai a nemi ruwa masu kyau misalin lita 3 a saka a tukunya a tafasa na a qalla mintuna 30 a bari sai ya tafasa sosai ake bukata.
Sai a sauke a tace da kyau a saka a galam a ajiye za a rinka shan glass daya da safe , daya da dare,a kalla Sau uku a cikin sati.
Ba fa kullum za a sha ba.

Magani ne na

Cutukan bladder
Kamar yawan yin fitsari ba kakkautawa,rashin iya riqe fitsari na lokaci,kaikayin matse matsi, toshewar bladder kanta,rashin samun iya fitsari ko jin ciwo da zarni a yayin fitsari da kuma masu fitsarin jini.

Yana wanke dattin ciki daga qazanta ta cikin hanji da suka taru.

Yana daidata al’ada ga mata masu matsalar rikicewar haila

Yana bude jiyojin bladder da suka toshe.

Yana wanke dattin babbar hanza (colon)

Yana maganin yawan tusa da saurin lalacewar ciki.

Yana magance yawan kumburin ciki da tsamin ciki.

Yana wanke mahaifa ga maccen da ta samu miscarriage.

Yana maganin bayan gari mai tauri mai fita da qyar a yayin toilet.

Yana qarawa hanjin ciki lafiya sabili da wankewar qazanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *