A MATSAYINKI NA DIYA MACE YA KAMATA KISAN WANNAN

  1. Ita diya mace da kunya da kawaici akasanta dashi.
  2. sannan mace tana da Aji,shi kalman Aji bakowace mace bane take gane ya kalman Aji yake ba,saboda da dama wasu matan sukanyi wulakanci wai suna nufin su a hakanne aji.
  3. A matsayin ki na mace tara samarika barkatai kowa naki ne hakan gaskiya babu mutunci,
    ki tsaida mutum nagartacce wanda kika yarda da tarbiyyan sa.idan har da gaske yake to ya fito a tsayar da magana.
  4. daga lokacin daki ka ga Al’adun saurayin bana kirki bane,kiyi gaggawan rabuwa dashi tun kafin ya bata miki rayuwa.
  5. ko kinsan cewa nuna kwadayinki shi zaima saka a lalata miki rayuwa?
  6. karki yarda ma ki biyewa saurayin dazai fara biki zancen batsa,
    mutum mai kaunar ki da gaskiya ko kadan bazai taba shigo miki da zancen banza ba.
  7. karki yarda dawani dadin bakin saurayi yana lallaba ki akan zai aure ki ya cutar miki da rayuwa,idan ya cuce ki bazai taba auran ki ba gudun ki zaiyi,
    idan kinga saurayi ya shigo da takunsa na son bata ki koreshi da hanzari ki kyaleshi kuma sai kinga ubangiji ya baki wanda yafi shi komai.
  8. kina mace ki tsare mutunci sosai,kisan kuma mutanen dazaki dinga mu’amula dasu,
    sannan kina budurwa ki dinga taimakawa mahaifiyarki da ayyukan gida,
    akwai yan matan dabasa son taimakawa mahaifiyarsu da ayyukan gida sai dai su zauna suna kallon ta.

Wannan sakon na ‘yan mata ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *