YADDA AKE SOYAYYAR TALIYA

 
Abubuwan Da Ake Bukata

Taliya
Tumatir
Nama
Kaza
Karas
Koren wake
‘peas’
Magi
Kori
Tafarnuwa
Citta
Albasa

YADDA AKE WANNAN HADIN

A dora ruwa a wuta, bayan ya tafasa sannan a zuba taliya da gishiri kadan. Idan ta yi tafasa daya sai a tsame. A dora man gyada a wuta sannan a zuba yankakkiyar albasa da yankakken tumatir da jajjagaggen attarugu. A tafasa nama sannan a yayyanka shi kanana sannan a zuba. A zuba magi, kori da garin tafarnuwa da citta sannan a dauko wannan taliyar a zuba ta a ciki a gauraya. A zuba ruwa kadan sannan a rufe bayan mintuna biyar a sauke.

A tafasa kaza ta yi laushi hade da magi da kayan kanshi sannan a soya da man gyada. A soya tumatir da attarugu da albasa. A zuba magi da citta da tafarnuwa. Bayan sun soyu sannan a dauko kazan a cakuda shi a ciki sannan a dora a kan wannan soyayyar taliyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *