πππππ πππππ ππ ππππππ ππππ πππππ ππππ ππ ππππ
Mace tana son namiji mai tausayi ba mai kaushin zuciya ba da saurin duka. Tana son mutum ya zamo ko faΙa zai mata ya yi cikin hikima.
Sanan kuma mace tanaso namiji mai son addini da sanin yakamata
Mace tana son wanda zai girmama ta ba wanda zai tozarta ta da gori ba.
Mace tana son namiji ΖaΖΖarfa mai lafiyar da zai biya mata buΖatar ta aure.
Mace tana son namijin da yake amsa kuskurensa idan ya aikata.
Tana son namiji mai karamci, alheri ba ΖanΖamo ba.
Mace tana son namijin da ya yarda da kansa da soyayyarsa.
Kuma Ba ta son namiji mai nauyin jiki da kasala wanda zai ta wahalar da ita.
Mace tana son namijin da zai sa ta farin ciki ta ji cewar ta cika mace. Ba wanda in ya doso gida za ta dinga fargaba ba, ba za ta sake walwala ba sai ya fita.
Tana son namijin da ke son ta don Allah ba don dukiya, matsayi ko kyanta ba. Domin ta san idan waΙannan abubuwa suka Ζare watsar da ita zai yi.
Mace tana son namiji mai wayo kuma mai haΖuri.
Tana son namiji mai dogon tunani kafin ya yanke hukunci. Wanda ko rai ta Ιata masa ba zai yanke hukunci ba sai ya yi tunani.
Mace tanason namijin da xai kasance mata abokin wasa waddda zai rika tayata aiki yayin da yake free a gida
FATAN ZAKA KASANCE HAKA GA MATARKA